Game Da Mu

Suna na Radiyon Talaka, kuma nine Radiyon Jama’a na ainihi akan yanar gizo. Ina baiwa Talaka damar bayyana muryarsa, damuwarsa, da ra’ayoyinsa. Burina shine bunkasa rayuwar talakawa, da basu bayanai ingantattu da kuma kwatar musu hakkin su.

Bello Galadanchi PhD ne tare da aminin sa Usman Ahmad Kabara suka kirkiro ni bayan share sama da shekaru shida suna shiri. Duka iyaye na su biyu kwararrun ‘yan jarida ne, wadanda suka yi aiki tare a gidajen radiyon kasashen waje, da ma na arewacin Najeriya. Sun yi alwashin ilimintar da ku, fadakar da ku da ma nishadantar da ku.

Zan kawo muku shirye-shirye ta yin amfani da sauti, da hotuna, da bidiyo da ma rubutattun labarai. Zan ji dadi idan kuna bada gudunmuwa wajen bayyana ra’ayoyinku, ko fashin baki, ko ma yi mun tsokaci akai akai.

Karin bayanai dangane da ayyuka na, da lokutan da zan fara gabatar da shirye-shirye na nan tafe.


Wanda Suka Kafa:

Bello Habib Galadanchi (PhD)

Dan asalin ƙasar Amurka da Tarayyar Nijeriya, dan jarida ne, marubuci kuma mai shirya fina-finai. Bello Galadanchi, ya yi wa kansa suna bayan ya lashe lambobin yabo da yawa a wasu gajerun fina-finai a duniya. Kafin daga baya su hada hannu da Usman Kabara don kafa abin da suke ganin zai amfani rayuwar talakawa a kasashenmu.

Usman Kabara Ahmad

Haifaffen unguwar Kabara a birnin Kano amma girman Kaduna duk a Najeriya, kuma mazaunin kasar Amurka. Kwararren Dan Jarida ne da ya yi ayyuka a kafofin labaran gida da kasashen waje kafin kafa gidan Radiyon Talaka.

Ma’aikatanmu:

Bello Galadanchi – Babban editan labarai da al’amuran yau da kullum

Usman Kabara – Babban editan shirye-shirye Da rahotannin musamman

Mufeeda Rasheed – Jami’ar shafukan sada zumuntar yanar gizo

Abubakar Sadiq – Editan labarai da rahotanni

Sashen mu na Instagram:

Instagram has returned empty data. Please authorize your Instagram account in the plugin settings .