Majalisar zartarwa ta kasa, ta amince da sakin sama da Naira Biliyan 44 domin bada kwangilar samar da tituna a birnin Abuja.

Aikin wanda zai gudana a ƙarƙshin ma’aikatar kula da birnin da ma’aikatar ayyuka da gidaje, ya ƙunshi inganta samar da ruwan sha da samar da tituna a sassan birnin.

Rahotanni sun ambato ministan yada labarai Lai Muhammad ya na cewa, an amince da sakin Naira Biliyan 31 da Miliyan 630 da dubu 221 da 349 a kan ayyukan.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunda Fashola, ya ce ma’aikatar shi ta haɗa hannu da hukumar kula da ingancin tituna ta FERMA, domin tabbatar da an yi aikin yadda ya kamata, wanda ya ce zai lakume naira Biliyan 8 da miliyan 180 da dubu 948 da 137 da Kobo 50.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *