Rahotanni na cewa, ‘yan bindiga sun hallaka mutane biyar, ciki har da ‘yan sanda uku a gidan shugaban Karamar Hukumar Katsina-Ala Alfred Avalumun Atera da ke Jihar Benue.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa, an kuma jikkata mutane da dama yayin harin da aka kai da misalin karfe 11:30 na safe.

Rahotanni sun ce, lamarin ya janyo tashin hankali a yankin, kafin daga bisani ‘yan sanda su ka shawo kan sa.

Jami’in yada labarai na ƙaramar hukumar Tertesa Benga ya tabbatar wa manema labarai faruwa lamarin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *