Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya ce ba ya da niyyar rufe jihar sa a matsayin matakin dakile yaduwar annobar korona karo na biyu.

Lalong ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da masu ruwa da tsaki ciki har da shugabannin kananan hukumomi da  sarakuna da shugabannin addinai da hakimai da kuma kwararru a fannin lafiya domin tattauna yadda za a magance lamarin.

A cikin wata sanarwa daga daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan Mecham Makut ya fitar, ya ce sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin yaki da annobar Farfesa Danladi Atu ne ya jagoranci taron.

Atu ya ce an shirya taron ne, domin janyo hankalin masu ruwa da tsaki don magance annobar cikin gaugawa musamman a lokacin Kirsimeti.

Ya ce gwamnan ya yi umurnin daukar tsatsauran matakai domin tabbatar da ganin an wayar da kan mutane don kiyaye dokokin korona tare da dakile yaduwar ta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *