Gwamnatin jihar Borno, ta ce an gano ma’aikatan bogi dubu 25 da 56 a matsayin malaman makaranta da ma’aikatan ƙananan hukumomi.

A cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, gwamnatin ta ce an gano hakan ne, bayan umarnin da Gwamna Zulum ya bada na yin binciken tantancewa har sau biyu.

Kwamitoci biyu na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi da na malaman makaranta ne su ka gabatar da rahoton binciken nasu ga gwamnan.

Daga cikin jimillar ma’aikatan Bogi  dubu 14 da 762 su na karɓar albashi ne a matsayin ma’aikatan ƙananan hukumomi, yayin da dubu 7 da 794 kuma malaman makaranta ne na bogi.

Sanarwar ta ce, gwamnati ta yi nasarar samun rarar naira miliyan 420 kamar yadda bayanan da gwamna ya gabatar su ka nuna.

Naira miliyan 183 da dubu 600 an same su ne bayan dakatar da biyan ma’aikatan bogi na ƙananan hukkmomi, yayin da aka samu naira miliyan 237 da ake biyan malaman makaranta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *