Wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar dan shekaru 50 ya kashe kan sa ta hanyar rataya a jihar Kano.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Alhamis da ta gabata, a shagon sana’ar sa da ke kan titin Zoo road.

Makwaftan shagon marigayin, sun ce tare da shi su ka gudanar da sallar la’asar, daga bisani su ka ji labarin rasuwar sa bayan wasu abokan kasuwancin sa sun ankara da halin da ya ke ciki a cikin shagon shi.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa, marigayin bay a da wata lalurar damuwa ko tabin hankali kafin rasuwar sa.

Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin, kamart yadda kakkakin ta DSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *