Shelkwatar tsaron Nijeriya, ta ce sojoji sun bindige mahara masu garkuwa da mutane kimanin 108 a yankin Arewa maso Yamma da kuma burbushin wasu ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabashin Nijeriya cikin mako guda.

Kakakin hukumar Tsaron Nijeriya John Enenche ya bayyana haka, yayin da ya ke bada bayanin nararorin da sojoji su ka samu a Abuja.

Manjo Janar Enenche, ya ce Dakarun Operation Hadarin Daji sun gudanar da hare-haren sama da kasa da kuma yin rubdugun ruwan wuta a wasu sansanonin ‘yan bindigar da aka yi wa takakki aka kifar da su baki daya a yankin arewa maso yamma.

Ya ce bayan a kashe mahara masu yawan gaske, an kuma kama wasu tare da munafukai da magulmatan da ke hada kai da su, su na ba su rahotannin mutanen da za su kama su yi garkuwa da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *