Wata babbar kotu da ke a Abuja, ta bada belin Sanata Ali Ndume bayan ya kwashe kwanaki biyar a gidan yari, sakamakon kasa gabatar da Abdurasheed Maina da ake zargi da almundahanar kudaden fansho.

Mai shari Okon Abang, ya ce kotun ta yi amfani da karfin ikon ta ne saboda dottakon da Sanata Ndume ya nuna a lokacin da ake gudanar da shari’ar Maina, wanda ya tsaya ma shi a matsayin mai karbar beli.

Alkali Abang ne ya bukaci a tura Sanatan zuwa gidan yari, da kuma asarar gidan sa da ya kai miliyan 500 sakamakon gazawa wajen gabatar da wanda ya karbi belin sa a shari’ar da ake yi.

Sanata Ndume, ya ce ya dauki matsayin tsaya wa Maina ne saboda bukatar kotu na ganin an gabatar da mai rike da mukamin Sanata, kuma ganin ya fito daga mazabar sa ne ya sa ya gabatar da kan sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *