Gwamnatin tarayya ta ce za ta ba talakawa masu sana’o’i tallafin kudade a jahohi 12.

Gwamnatin tarayya za ta bada tallafin ne ta hannun gwamnatocin jahohin, a ci-gaba da tsarin bada tallafi ga masu sana’o’in hannu da gwamnatin ta fara a watan Satumba.

Ya zuwa yanzu dai, jihohi 12 masu dubban mutanen da ke da kananan sana’o’i ne suka amfana a karon farko daga cikin Naira biliyan 75 da aka ware.

Shirin tallafin, ya na daga cikin wata hikima da gwamnati ta bullo da ita domin karfafa gwiwar masu kananan sana’o’i don su dogara da kan su, su kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan’uwan su matasa masu neman aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *