Gwamnatin tarayya ta ce kananan hukumomi 38 ne kacal suka yi nasarar magance matsalar yin bayan gida a bainar jama’a daga cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya.

Ministan kula da albarkatun ruwa Suleiman Adamu ya bayyana haka lokacin da ya ke kaddamar da shirin rungumar amfani da ban daki wajen biyan bukata.

Suleiman Adamu, ya ce shirin da aka kaddamar na ganin ana amfani da bayan gida ya samu nasara, inda kananan hukumomin da suka rungumi shirin wajen hana biyan bukata a bainar jama’a suka tashi daga 16 zuwa 38 a shekarar 2019.

Ministan ya ce yanzu haka wasu karin kananan hukumomi 6 na kan hanyar samun irin wannan nasarar duk da matsalolin da aka fuskanta bana na annobar korona.

Domin yabawa kananan hukumomin da suka samu nasara, ministan ya ce za’a fifita su wajen gabatar da ayyukan samar da ruwan sha na gwamnatin tarayya a cikin su.

Adamu ya bayyana damuwa kan yadda wasu jihohi suke kau da kai daga daukar matakin dakile wannan mummunar dabi’a wadda ke da matukar illa wajen kula da lafiyar jama’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *