‘Yan majalisar Dattawa sun amince da buƙatar Shugaba Muhammad Buhari, ta neman a biya Naira biliyan 148 da miliyan 141 da dubu 969 da 161 da kobo 24 ga jihohin Ondo da Osun da Rivers da Bayelsa da kuma Cross River.

Kuɗaɗen dai na biyan bashin kwangilolin da su ka aiwatar ne a jihohin su a madadin gwamnatin tarayya.

Amincewar Sanatocin, ta biyo bayan duba da ƙorafin da kwamitin basussukan cikin gida da waje na majalisar dattawa a karkashin jagorancin Sanata Clifford Ordia.

Clifford Ordia, ya ce yawancin manyan titunan tarayya a jihohin da za su ci moriyar kuɗaɗen, jihohin ne su ka zuba kuɗaɗen su kafin gwamnatin tarayya ta kai masu dauki.

Ya ce ma’aikatar ayyuka ta kai ziyara akai-akai zuwa titunan tarayya da jihohin su ka kammala, domin dubawa ko sahihacin aikin ya kai nagartar da ake buƙata.

Sai dai Sanatan ya ce, jihohi irin su Cross River da Rivers da Bayelsa da Ondo sun fara ayyukan tun cikin shekara ta 2005 zuwa yau.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *