Gwamnonin kudu maso kudu sun koka a kan rashin ci-gaban yankin su, inda su k ace da dukiyar yankin su ake bunkasa sauran yankuna.

Shugaban gwamnonin Ifeanyi Okowa ya bayyana haka, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari su ka yi.

Abubuwan da su ka tattauna a wajen taron, ya na kunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan jihar Rivers ta fuskar yada labarai Kelvin Ebiri ya fitar.

Yayin da yak e jawabi a wajen taron, wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal, Okowa ya ce ya kamata a ba jihohin yankin su damar amfana da ma’adanan su domin taimaka wa ‘yan asalin yankin.

Ya ce sun san irin albarkar da kasar nan e da ita, don haka wajibi ne a ba jihohin dama ta yadda za su taimaki kan su da kan su.

Gwamna Okowa ya cigaba da cewa, abu mafi muni shi ne yadda wasu ‘yan Nijeriya ba su fahimta ko kuma tausayin yankin kudu-kudu, musamman a kan yadda ya ke a lalace, don haka ya ce su na bukatar ba yankin damar amfani da ma’adanai da sauran kayan alatun da ke wajen don ciyar da yankin gaba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *