Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce akwai yiwuwar Gwamnatin tarayya ta sake bude iyakokin Nijeriya da aka rufe tun watan Agustan shekarar da ta gabata.

Yayin wani taron tattalin arzikin Nijeriya da ya gudana a Legas, ta ce kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin duba ribar rufe iyakokin sun ba shi shawarar ya bude iyakokin.

Ta ce ta na kyautata zaton cewa shugaba Buhari zai dauki shawarar ya kuma aiwatar da ita nan ba da dadewa ba.

Ministar ta kara da cewa, dukkan ‘yan kwamitin sun bada shawarar cewa lokacin bude iyakokin yayi, don haka ta ce su na

sa ran a bude iyakokin nan ba da dadewa ba.

Nijeriya dai ta rufe iyakokin ta na tudu ne a watan Agusta na shekara ta 2019, domin dakile shigo da makamai da miyagun kwayoyi da kayan masarufi daga kasashe makwafta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *