Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola, ya ce ya zama wajibi a girmama tsarin karɓa-karɓa na jam’iyyar APC gabanin zaɓubbukan shekara ta 2023.

Fashola ya bayyana haka ne, yayin da wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja, inda ya roƙi shugabannin jam’iyyar APC su girmama yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓar da aka cimmawa a shekara ta 2015.

Maganar ministan dai ta na zuwa ne, bayan Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC Dr. Salihu Lukman, ya dage a kan cewa za a ba duk dan jam’iyya damar shiga takara a shekara ta 2023.

A wata hira da yay i da manema labarai, Lukman ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa cewa jam’iyyar APCn ta cimma yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *