Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa shugaban jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Philip Shekwo.

Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Lahadi a nan Abuja, inda ya ce dole ne a kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a Najeriya.

Ya ce shugaban kasa ya amince da shawarar Babban Sufeton ‘Yan Sanda Mohammed Adamu na kara aike wa da jami’an tsaro zuwa jihar.

Shugaban kasa ya jajanta wa iyalan marigayin bisa rashin sa, inda ya bayyana marigayin a matsayin dan kasa na gari.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe marigayin har sau biyu ne wanda hakan ya yi sanadin rasa ran sa da safiyar Lahadi, kwana daya bayan ‘yan bindiga sun sace shi daga gidan sa a Lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *