Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce tana kan bincike domin gano wadanda suka kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar, Philip Tatari Shekwo.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Ramhan Nansel, ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya bayar.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta zuba jami’an ta a cikin gari kana ta tabbatarwa al’ummar jihar cewa ba za a sake samun irin wannan danyen aikin ba kuma su kwantar da hankalin su.

ASP Ramhan Nansel, ya ce sai dai har yanzun basu samu wani bayani a kan dalilin da yasa aka yi garkuwa da shi kana aka kashe shi.

A daren ranar Asabar ne dai wasu ‘yan bindiga suka shiga gidan marigayin suka dauke shi, wanda daga bisani aka samu gawar sa a kusa da gidan sa.

Sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Aliyu Bello, da yake bayyana kaduwar su ya ce da farko sun dauka masu garkuwa da mutane damin neman kudin fansa, har ma suna tunanin yanda za su kubutar da shi, sai kwatsam aka tsinci gawar sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *