Wata babbar kotun tarayya, ta bada umurnin tsare Sanata Ali Ndume a gidan yarin Kuje, sakamakon kasa kawo tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Nijeriya garambawul Abdulrasheed Maina.

Sanata Ndume dai ya tsaya wa Maina ne aka bada belin sa, amma ya kasa bayyana gaban kotu domin ci-gaba da shiri’ar sa.

Wata majiya ta ce, Alƙalin kotun ya bada umurnin a tsare Ali Ndume har sai ya cika sharuɗɗan belin.

Haka kuma, Kotun ta umurci gwamnatin tarayya ta saida gidan Sanata Ndume da ke Asokoro domin fitar da kuɗin da aka ƙayyade na belin naira miliyan 500, sai dai Lauyan Sanatan ya ce za su kalubalanci hukuncin kotun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *