Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, ‘yan sandan da aka sace tsakanin Zamfara da Katsina sun kubuta.

Wasu majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun saki ‘yan sanda biyar da su ka sace bayan takwas daga cikin su sun riga sun tsere.

Bayanai sun nuna cewa, an kwantar da ‘yan sandan biyar a wani asibiti da ke Gusau ana duba lafiyar su.

Tun farko dai majoyoyi sun tabbatar da cewa, ‘yan sanda 12 masu mukamin ASP  ne‘yan bindigar su ka sace a wani kauye da ke tsakanin jihohin Katsina da Zamfara.

Sai dai wasu manyan majiyoyi daga gwamnatin jihar Zamfara sun tabbatar wa manema labarai cewa, wasu daga cikin su sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *