Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karɓi rahoton kwamitin sauraren ba’asin zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Mai shari’a Ayo Salami ne ya miƙa rahoton kwamitin ga shugaba Muhammadu Buhari, kuma ya gabatar da rahoton ne a cikin wasu akwatuna huɗu maƙare da hujjoji a kan zarge-zargen da ake yi wa Ibrahim magu.

Mai shari’a Ayo Salami, ya ce sun samu shaidu akalla 113 da su ka gabatar da bayanai a gaban kwamitin ciki har da Magu, da wasu ƙorafe-ƙorafe 46 daga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi a kan Ibrahim Magu da hukumar EFCC.

Sai dai wani abin jan hankali game da rahoton shi ne, shawarar da kwamitin ya bada na rage yawan ‘yan sandan da ke yi wa hukumar EFCC hidima.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce Shugaba Buhari ya yi umarnin a yi gwanjon kayayyakin da hukumar EFCC ta ƙwato daga hannun waɗanda ake zargi da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta duba shawarwarin da aka bada musamman yadda ta ɗauki aniyar yaƙi da cin hanci da rashawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *