Gwamnatin jihar Kaduna, ta dakatar da shugaban kwamitin masu zaben sarkin Zazzau Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu.

Wata majiya ta ce, an gargadi Iyan Zazzau da sauran ‘yan kwamitin zaben sarkin uku su canza lauyan su zuwa lauyan gwamnati a karar da su ka shigar kotu, a kan nadin Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Idan dai ba a manta ba, Iyan Zazzau ya shigar da kara kotu ya na kalubalantar nadin Ahmad Bamalli matsayin sabon sarkin masarauta Zazzau.

A wata wasika da babban sakataren ma’aikatar harkokin kananan hukumomi ya sanya wa hannu a madadin kwamishanan, Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da Wazirin Zazzau.

Daga cikin wandanda aka aike wa takardar akwai limamin Zazzau da Wazirin Zazzau da Limamin Kona da Makama Karami a kan rashin halartar wani taro da aka yi na shirin bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *