Ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Jamus, ya dakatar da wani ma’aikacin sa bisa zargin yunƙurin lalata da wata mace a birnin Berlin.

Jakadan Nijeriya na kasar Yusuf Tuggar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Matakin dakatarwar, ya biyo bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta da ke nuna wani ma’aikaci da aka ce mai gadi ne, ya na neman yin lalata da wata mata a matsayin ladar yi mata fasfo.

Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce ofishin jakadancin Nijeriya ba zai taɓa amincewa da halin rashin ɗa’a ba.

Ya ce ba za su taɓa lamuntar yin amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba, musamman wajen aikata lalata. Mun fara bincike kan lamarin lalata da kuma duk wani abu da ya faru,” in jni shi.

Jakadan ya cigaba da cewa, ana gudanar da binciken ne a cikin sauri da kuma kulawar da lamarin ya ke buƙata, kuma idan aka kammala mai laifin zai fuskanci hukunci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *