Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, ta ce ta kama wasu ‘yan bindiga 15 tare da kwato shanu da tumaki 495.

Jami’an tsaro dai sun samu nasarar dakile ayyukan ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomi 8, inda ayyukan maharan su ka fi kamari a jihar Katsina har su ka kama wasu daga cikin mayakan da madugun su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina Gambo Isah, ya ce bisa ga wasu sahihan bayanan sirri da su ka samu, shugaban ‘yan sandan karamar hukumar Dutsinma ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa kauyen Tsaunin Bala a karamar hukumar Danmusa, inda su ka samu nasarar kama mutane 11 da jagoran su Alhaji Adamu, wanda aka fi sani da lakabin ‘SHANTAL’, tare da kwato dabbobi 185 da su ka hada da tumaki 54.

A wani bangare kuma, shugaban ‘yan sanda na karamar hukumar Batsari, ya jagoranci sintirin da ake kira “Operation Puff Adder” da na Sharar Daji” da tawagar ‘yan banga daga yankin Dankar zuwa kauyen Dangayya, inda su ka kama wasu mutane 3 aka kuma yi nasarar kwato shanu 43 da tumaki 213 da ake kyautata zaton na al’ummar yankin ne aka sace.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *