Kwamitin da gwamnatin jihar Lagos ta kafa domin binciken masababin mutuwar wasu mutane yayin zanga-zangar #EndSARS, ya saurari bahasi daga kwamandan rundunar soji da ake zargi da bude wa masu zangar zangar wuta.

Da ya ke bada bahasi a gaban kwamitin, Kwamandan Bataliya ta 81 na Rundunar sojin Nijeriya Brigadiya Janar Ahmed Ibrahim Taiwo, ya musanta yin amfani da karfin soji a kan masu zanga-zanga a kofar Lekki, inda hukumar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce an kashe mutane goma.

Brigediya Janar Taiwo, ya ce wabiji ne sojoji su shiga lamarin domin kare rayuka da kadarorin al’umma idan aka samu yanayi na rudani da tashin hankali.

Ya ce an nemi taimakon sojojin ne bayan lamarin ya wuce kima, inda aka rika barnata kaddarorin jama’a da kuma kwasar ganima, ya na mai cewa, duk duniya ana neman taimakon soji idan aka shiga wani hali da ya fi karfin ‘yan sanda da masu kwantar da tarzoma.

Janar Ahmed, ya bayyana takaicin ganin yadda jama’a su ka shiga wasoson dukiyar wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *