Gwamnatin Tarayya ta saki sakamakon jarrabawar kammala karatun firamare.

Jarrabawar dai, da ita ne ɗalibai za su samu damar shiga kwalejojin Gwamnatin Tarayya 110 da ake kira Unity Schools a faɗin ƙasar nan.

Ɗalibi dubu 92 da 591 ne su ka yi rajistar jarrabawar da aka yi ranar 17 ga watan Oktoba, amma dubu 70 da 580 ne su ka rubuta, yayin da dubu 16 da 714 ba su zauna ba.

Da su ke gabatar da sakamakon a Abuja, shugaban hukumar NECO Godwill Obiom da Ministan Ilimi Adamu Adamu, sun ce an gudanar da jarrabawar salin-alin a ƙarƙashin kulawar masu sa-ido na ciki da wajen hukumar.

Ɗalibin da ya fi ƙoƙari ya fito ne daga Jihar Anambra da maki 199 cikin 100, na biyun kuma daga jihar Imo da maki 198, sai kuma na uku daga jihar Ogun da ya samu maki 197.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *