Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce za ta tallafawa cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, domin yakar cutar shawara a jihohin Delta da Enugu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun jami’inta dake kula shiyyar Afrika.

Sanarwar ta ce hukumar za ta taimakawa cibiyar wajen bincike tare da samar da magunguna da za su taimaka wajen yakar cutar baki daya.

A ranakun 2 da 3 ga watan nan ne hukumomin lafiya a jihohin suka sanar da hukumar NCDC bullar cutar kan wasu da suka nuna alamu a jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *