Hukumar zabe mai zaman kantar ta kasa INEC, ta bukaci hadin kan kafofin yada labarai wajen tabbatar da sahihin zabe a fadin Najeriya.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar Ahmed Mu’azu, ya bukaci hakan a Abuja, a wani taro da ya yi ta fasahar zamani da manema labarai a Abuja.

Mu’azu ya yabawa irin rawar da kafofin yada labaran suka taka a zabubbukan da suka gabata a jihohin Edo da Ondo, bisa namijin kokari wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

Ya ce akwai taro da za a rika shiryawa lokaci zuwa lokaci domin tattaunawa kan zabubbukan cike gurbi 15 da aka dage a jihohi 11 dake fadin kasar nan.

Hukumar ta dage taron da ta yi ninyar gudanarwa a ranar 31 ga watan da ya gabata, sakamakon barazanar tsaro biyo bayan zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

A nasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan jaridu na kasa Chris Isinguzo, ya ba hukumar tabbacin cewa ‘yan jaridu za su ci gaba da tallafawa a zabubbukan dake tafe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *