Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe sama da naira billiyan 62 a aikin babbar hanyar Kano, Dawakin Tofa, Gwarzo zuwa Dariyo.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya ce gwamnatin tarayya na sa ran kammala aikin hanyar ne a cikin shekaru 2.

A lokacin taron ministan kula da harkokin yada labarai da al’adu Lai Muhammad ya gabatar da wasu takardu na ministan kula harkokin sufurin jiragen sama da kuma na kasuwanci da harkokin zuba jari.

Mohammed ya ce majalisar ta amince da kashe sama da naira milliyan dari 4 da 70, domin sayo wasu kayayyaki da sanya su tare da kaddamar dasu a filin jirgin sama na Lagos.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *