Kwamitin kula da harkokin aikin soji na majalisar wakilai ya yabawa gwamnatin jihar Gombe bisa namijin kokari da take na tabbatar da tsaro a yankin na Arewa Maso Gabas.

Shugaban kwamitin Abdulrazak Namdas, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci gwamitin kaiwa gwamnan jihar Inuwa Yahaya ziyara a jihar.

Namdas ya ce kwamitin ya gamsu da irin goyon baya da gudunmawar da jami’an tsaro ke samu daga gwamnatin jihar domin tabbatar da tsaro a yankin.

Ya ce duk da cewa kwamitin nasu na kula da harkokin soji ne kawai, ya lura da irin gudunmawar da gwamnatin ke ba sauran hukumomin tsaro dan tabbatar da zaman lafiya.

Sannan ya bukaci gwamnatin tarayya ta maida hankali wajen horas da jami’an ‘yan sanda da kuma basu kayayyakin aiki na zamani domin a cewarsa hakan zai ragewa jami’an soji aiki.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Inuwa Yahaya, ya ce gwamnatin jihar na da kyakkyawar alaka da hukumomin tsaro, kuma gwamnatinsa na basu goyin baya ne saboda sanin muhimmancinsu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *