Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilai Akeem Adeyemi, ya bukaci bayani kan karin da aka samu na kasafin kudin shekarar 2021 a ma’aikatar kimiyya da fasahar zamani.

Adeyemi ya bayyana hakan ne a lokacin da hadakar kwamitocin majalisar ke tattara bayanai kan kasafin kudi da aka warewa wasu ma’aikatu a Abuja.

Ya ce bangaren sadarwa na da matukar muhimmanci musamman ma idan aka yi amfani da kwarewa wajen gudanar da aiki tare da yin abubuwan da suka kamata.

A nasa jawabin ministan sadarwa da fasahar zamini Isa Ibrahim Pantami, ya ce karin kasafin kudin ya kunshi aikace-aikacen da ake na rijistar zama dan kasa a hukumar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *