Majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatin tarayya ta janyo matasa tare da tattaunawa da su biyo bayan zanga-zangar adawa da rundunar SARS da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mataimakiyar shugaban majalisar Amina Mohammed ta mika bukatar a lokacin da ta ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.

Amina ta kuma bukaci gwamnatin shugaban kasa Buhari da ta maida hankali wajen gudanar da ayyuka kamar yadda ya alkawarta a baya domin ya samu yaddar ‘yan Najeriya.

A dake maida martini, shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci matasa da su rungumi zaman lafiya, wanda a cewarsa shine kadai abin da zai amfane su a yanzu da kuma nan gaba.

Ya ce duk da cewa gwamnatinsa ta karbi mulki ne a lokacin da aka lalata abubuwa, akwai shirye-shirye da suke dashi na kara inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da ababen more rayuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *