Gwamnonin yakin kudu maso gabashin Najeriya sun gargadi al’ummar kabilar Igbo, musamman ‘yan kasuwa da su guji danganta kansu da haramtacciyar kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawar da suka yi A Port Harcourt babban birnin jihar Rivers, ciki har da gwamnan jihar Nyeson Wike.

Gwamnonin karkashin jagorancin shugaban gwamnonin yankin David Umahi, wanda shine gwamnan jihar Ebonyi, sun tattauna kan hanyoyin ci gaba da samun zaman lafiya a yankin.

Shugaban kungiyar Ohaneaze John Nnia Nwodo, ne ya jagoranci sauran ‘yan kungiyar a ganawar da aka yi da gwamninin biyo bayan rikici da aka samu da yayi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi a karkashin zanga-zangar adawa da rundunar SARS.

Umahi ya gargadi ‘yan kabilar Igbo da su nesanta kawunansu da haramtacciyar kungiyar, wanda a cewarsa ke neman jefa Najeriya cikin yakin basasa.

Ya ce sun kira taron ne domin bincike kan rahotanni dake yawo a shafukkan sada zumunta na zargin kashe ‘yan kabilar Igbo a jihar ta Rivers.

Umahi ya ce bayan bincike da suka gudanar sun gano cewa babu kanshin gaskiya a labaran da ake ta yadawa a kafofin yada labaran.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *