Gwamnatin jihar Niger ta ce gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya kamu da cutar korona.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Mary Noel-Berje.

Ta ce gwamnan ya tabbatar da haka a shafinsa na twitter, inda tuni ya kebance kansa, tare da karbar magunguna kamar yadda kwararru kan yaki da cututtuka suka bukata.

Marry ta bukaci al’ummomin jihar daman a kasa baki daya da su taya gwamnan da addu’a dan ganin ya samu lafiya, tare da komowa bakin aiki.

Sannan ta bukaci al’ummomi da su ci gaba da daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar.

A baya dai gwamnonin da suka hada da na Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, Ondo Kayode Fayemi sun kamu da cutar inda suka warke bayan daukar tsawon lokaci da suka yi a kebe.’

Sauran gwamnonin da suka kamu suka kuma warke sun hada da Seyi Makinde na jihar Oyo, Bala Muhammad na jihar Bauchi, Ifeanyi Okowa na jihar Delta da kuma Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *