Mai rikon mukamin kwamandan runduna ta  dake yaki da ayyukan ta’addanci a Maiduguri Abdul-Khalifa Ibrahim, ya yabawa bataliya ta  na rundunar soji bisa kokarin da suke na yakar ayyukan ta’addanci.

Ibrahim wanda shine kwamandan wani sashe na rundunar Operation Lafiya Dole, ya yabawa jami’an sojin ne a wani taro na musamman da aka shiryawa jami’an dake yaki da ‘yan Boko Haram.

Ya ce jami’an sojin sun bada gudunmawa wajen tabbatar da tsaro a garin Gwoza, inda daga bisani ‘yan Boko Haram suka sake kai hari bayan sojojin sun bar garin, wanda nan take sojojin da suka rage suka suka dakile harin.

Kwamandan ya bukace su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, musamman a yanzu da suke barin fagen daga inda za su koma wajen iyalansu da sauran mutane.

Ya ce bayan sun samu hutu na dan wani lokaci a gidajensu rundunar sojin Najeriya za ta tura su wurare da za su karo karatu da kuma kwarewa kan aiki, inda daga bisani za a kara musu girma.

A nasa jawabin daya daga cikin jagororin sojin Olarenwaju, ya nuna farin cikinsa bisa yadda suka kammala aikin dake gabansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *