Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutane 22, tare da bashi wa’adin watanni shidda ya saida Kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya sanar da haka yayin rantsar da kwamitin, inda ya ce tun a ranar 27 ga watan Oktoba na shekara ta 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ‘yan kwamitin.

Ya ce an zakulo ‘yan kwamitin ne daga hukumomin gwamnati da ke da alaka da yaki da cin hanci da rashawa, kuma babban mai nazarin shari’o’i a matakin tarayya Dayo Apata ne aka zaba a matsayin shugaban kwamitin.

Malami ya kara da cewa, daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai gaggauta saida Kadarorin da aka kwato domin gwamnati ta samu kudaden shiga.

Ya ce aikin su shi ne tabbatar da saida dukkan kadarorin gwamnati da aka kwato tare da saida su a cikin Nijeriya don gwamnati ta samu kudin shiga cikin gaugawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *