Ƙungiyar Kare Muradun Musulmin Nijeriya MURIC, ta ja hankalin ‘yan Nijeriya, musamman Musulmi su guji jefa kan su cikin wata sabuwar zanga-zangar #EndSARS da ake rade-radin din sake tadowa.

Shugaban kungiyar Ishaq Akinbola ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce MURIC ba ta goyon baya, kuma ta na ba ‘yan Nijeriya musamman Musulmai shawara kada su shiga zanga-zangar kwata-kwata.

Ya ce Kowa ya shaida irin mummunar barnar da ta biyo bayan zanga-zangar #EndSARS da aka yi, don haka ya ce ba su goyon bayan sake tada wata tarzoma a Nijeriya.

Ishaq Akinbola, ya ce doka ta amince da zanga-zanga idan ta lumana ce, amma muddin ta rikide zuwa tarzoma tabbas an wuce iyaka.

Ya ce tunda har gwamnatin tarayya ta amince za ta cika sharudda biyar da masu zanga-zangar su ka gindaya, ya kamata kowa ya jira ya ga abin da za ta yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *