Gwamnonin Jihohin Kudu maso Gabas na kabilun Igbo, sun sake jaddada aniyar ganin sun kara karfafa hadin kan Nijeriya tare da ci-gaba da dunkulewar kasar nan wuri guda.

Sun jaddada haka ne a wani taro da su ka yi a Enugu, inda su ka ce lallai Nigeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya shi ne mafi alheri, tare da kaunar juna da adalci da kuma rashin nuna son zuciya.

Bayanin dai ya na kunshe ne a cikin wata takardar jawabin bayan taro da su ka gudanar, inda su ka bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi duba ga irin bukatu da korafe-korafen da ‘yan yankin kudu maso gabas ke yi.

A cikin takardar, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas David Umahi na jihar Ebonyi, ya ce al’ummar Kudu maso Gabas sun yi amanna da kasancewar Nijeriya kasa daya dunkulalliya.

Ya ce al’ummuar  ta yi katutu a kowane yanki na kasar nan, wadanda sun yi gine-gine su na zaune lami-lafiya da yankin su na kasuwancin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *