Shugaban hukumar zabe mai zman kan ta ta kasa Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sauka daga kujerar sa, sannan ya mika ragamar shugabancin hukumar ga kwamishinan zabe na kasa Air Vice Marshal Muazu Ahmed mai ritaya.

Hakan dai, ya gudana ne a wajen wani taro da aka gudanar a helkwatar hukumar da ke Abuja.

Mu’azu Ahmed, zai yi aiki a matsayin Shugaban rikon kwarya na hukumar har zuwa lokacin da Majalisar dattawa za ta tabbatar da sake nada Farfesa Yakubu a matsayin shugaba.

Idan dai ba a manta ba, bayan shugaba Buhari ya kara zaben Yakubu, ya mika sunan sa ga majalisar tarayya domin tabbatar da shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *