Fadar Shugaban kasa ta ce, duk wadanda su ka bari zanga-zangar #EndSARS da ta yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi sai sun biya bashin abin da su ka aikata.

Mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana haka, yayin da ya bayyana a cikin wani shirin gidan talabijin na Channels ranar Lahadin dsa ta gabata.

Rahotanni sun ce, babban bankin Nijeriya ya rufe asusun mutane 20 da su ka jagoranci zanga-zangar #EndSARS, yayin da aka hana wata da ta daukaka gangamin Modupe Odele fita kasar waje a makon da ya gabata bayan hukumar kula da shige da fice ta kwace fasfon ta na shiga kasa da kasa.

Garba Shehu, ya ce akwai kundin tsarin mulki a karkashin sashe na 33, wanda ya ba al’umma ‘yancin yin zanga-zangar lumana, amma idan zanga-zangar lumana ta zama rikici akwai bukatar a yi aiki da doka da oda.

Ya ce kowa ya ga irin sace-sacen da aka yi na kayayyakin gwamnati da masu zaman kan su musamman a Lagos da Calabar da Filato da Taraba da birnin tarayya Abuja, don haka ya zama dole a bar doka ta yi hukunci a kan barnar da aka yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *