Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, ya ce ya naɗa Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau ne domin su gyara kuskuren cire Sarki Aliyu Ɗan Sidi da Turawan mulkin mallaka su ka yi.

El-Rufa’I, ya shaida wa sabon sarkin cewa, shekaru 100 kenan da cire kakan shi daga sarauta ba bisa adalci ba, ya na mai cewa, Gwamnan Mulkin Mallaka Herbert Symonds Goldsmith ne ya tsige Aliyu Dan-Sidi daga karagar mulki.

Yayin gudanar da bikin, sabon sarkin ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Sarkin Zazzau na 19, sannan Gwamna El-Rufa’i ya gabatar ma shi da ma’aikatan fadar sa.

Ya ce Allah Ya yi ma shi alfarma a matsayin shi na zaɓaɓɓen ma’aikacin gwamnati na farko da zai naɗa Sarkin Zazzau a dimokuraɗiyyance.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *