Rahotanni na cewa wata kotu a birnin Abu Dhabi na kasar Dubai, ta yanke ma wasu ‘yan Nijeriya shida hukunci bisa alaƙar su da ƙungiyar Boko Haram.

Wata majiya ta ce, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abu Dhabi, ta yanke wa biyu daga cikin su da su ka hada da Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Kotun, ta kuma yanke ma Ibrahim Ali Alhassan da AbdurRahman Ado Musa da Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa hukuncin daurin shekaru 10 kowannen su.

An dai zargi mutanen ne da laifin ɗaukar nauyin ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su kuɗaɗe.

Majiyar ta ce takardun shari’ar sun nuna wa, waɗanda aka ɗaure su na da hannu wajen tura wa Boko Haram kusan dala dubu 782 a tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2016.

Wani jami’in gwamnatin Nijeriya ya shaida wa manema labarai cewa suna sane da shari’ar, sai dai iyalai da abokan mutanen sun ce sharri aka yi masu, saboda sun daɗe su na yin harkar canjin kuɗaden ƙasashen waje.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *