An haifi Joseph Robinette Biden Jr. da aka fi sani da Joe Biden a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1942 a jihar Pennsylvania ta Amurka, sannan shine babba daga cikin ‘ya’ya 4 da iyayensa suka haifa sannan daga baya suka koma jihar Delaware da zama.

Bayan ya gama makarantar Firamare ne ya shiga Sakandare a inda a lokacin da ya ke karatun ya zama hazikin dalibi kuma gwanin buga kwallon kafar zari-rugar Amurkawa.

Ya karanci digirin farko a fannin tarihi da kimiyyar siyasa a jami’a inda daga baya kuma ya sake yin wani digirin a fannin shari’a ya kuma zama lauya.

Ya auri matarsa Neila Hunter a shekarar 1966 suka kuma haifi ‘ya’ya uku da suka hada da Beau da Hunter da kuma Naomi.

A shekarar 1970 aka zabi Joe a memba a majalisar karamar hukumar New Castle. Bayan shekara biyu kuma sai aka zabe shi a matsayin Dan Majalisar Dattawan Amurka daga jihar Dalaware 

A lokacin yana daga cikin Sanatocin da aka taba zaba da karancin shekaru a tarihin Amurka. Ya kuma kasance a matsayin Sanata har zuwa shekarar 2009.

Jim kadan bayan zaman Biden Sanata ne matarsa da ‘yarsa Naomi suka mutu a wani mummuman hatsarin mota, wanda shi ne ya ci gaba da renon ‘ya’yansa maza guda biyu da suka rage.

A shekarar 1977 ne ya sake aure da Jill Jacobs suka kuma haifi ‘ya mai suna Ashley. A shekarar 2016 Joe ya so tsayawa takarar neman shugabancin Amurka amma ya fasa saboda rasuwar dansa Beau a shekarar 2015.

Biden yayi zaryar hawa jirgin kasa har sau sama da sawu 8000 zuwa da komawa tsakanin garinsa na Wilmington ta jihar Delaware zuwa birnin Washington DC a lokacin da yake Sanata daga Litinin zuwa Juma’a.

Inda bayan Barack Obama ya zama shugaban kasar Amurka ya zabe Biden a matsayin mataimakinsa har tsawon shekaru takwas na mulkin da suka yi wa’adi biyu cikin dasawa da fahimtar juna.

A shekarar 2019 ne Joe ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin Amurka. Daga baya kuma ya zabi Sanata Kamala Harris wacce ruwa biyu ce da mahaifiyarta ‘yar Indiya ce mahaifinta kuma dan asalin tsibirin Caribbean. 

A ranar 7 ga watan Nuwambar shekarar nan ta 2020 ne aka tabbatar da samun nasarar lashe zaben Amurka da suka fafata da shugaba mai ci Donald Trump ya kuma buga shi da kasa a matsayin wanda za a rantsar a matsayin shugaban Amurka na 46 a watan Janairun shekara mai kamawa ta 2021.

Manufofin Joe Bidan :

  • Ilimi: Yana son tabbatar da cewa yara sun sami shiga makaranta tun daga matakin sharar fagen shiga firamare. Yana kuma son karawa malamai albashi da kara wa makarantu kudin tafiyarwa.
  • Kiwon Lafiya: Yana son inganta tsarin inshorar lafiya ta Obama care tare da tabbatar da kowa na iya samun kulawar lafiya da iya sayen magani cikin sauki.
  • Kudi da Haraji: Ya amince da cewa ya kamata masu hannu da shuni su fi kowa biyan haraji ba talaka ba.  Sannan yana son kashe kudade a kan ayyukan raya kasa kamar kyawawan hanyoyi, tsaftataccen ruwa sha da samun damar amfani da internet ga kowa. Da kuma bukatarsa ta yakar chanjin yanayi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *