Karshen tika-tika tik in ji bahaushe. Bayan kwanaki ana kidayar kuri’u a Amurka na neman tantance wanda zai lashe zaben shugaban kasar na ranar 4 ga Nuwambar 2020 da aka yi. Inda aka fafata tsakanin shugaban kasa mai ci yanzu na jam’iyyar ‘Republican’ Donal Trump da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na jam’iyyar ‘Democrat’.

A karshe dai Joe Biden ya lashe zaben a matsayin sabon shugaban kasar na 46 bayan ya kayar da shugaban kasar da ke kan mulki Donald Trump da kason kuri’un jihohin da ke da karfin tabbatar da wanda zai yi nasara da a ke kira ‘electoral college vote’ a turance. 

Dama kidayar wasu jihohi  guda hudu ne masu muhimmanci ya ja dadewar. Jihohin masu karfin wakilan kwalejin zaben da suka hada da Pennsylvania (kuri’a 20), Arizona (kuri’a 11), Georgia (kuria 16), Nevada (kuri’a 6), North Carolina (kuri’a 15) wadanda sune raba gardamar da a ka jira har zuwa tabbatar nasarar Joe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *