Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya bada umurnin janye jami’an da ke ba attajirai da manyan malamai da kamfanoni kariya a fadin kasar nan.

Umurnin dai, ya shafi mutane 60 da kamfanoni da coci-coci da Sanatoci sauran kungiyoyin addini da kuma masu hannu da shuni.

Daga ciki akwai Christ Embassy, Think Nigeria First Initiative, Uche Sylva International, Stanel Groups, da KYC Holding

Hakan ya na kunshe ne a cikin wasika da shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya aike wa dukkan kwamishanonin ‘yan sandan jihohin Nijeriya 36 da birnin tarayya Abuja.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 21 ga watan Oktoba ne, shugaban ‘yan sandan ya aika sakon waya ga dukkan kwamishanonin ‘yan sanda cewa su janye dogarawan daidaikun mutane, inda ya yi gargadin cewa duk wanda bai bi umurnin ba zai fuskanci hukunci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *