Ƙungiyar kare hakkin musulmi MURIC, ta bukaci a kama tare da gurfanar da Rev. Fr. Godfrey Igwebuike Onah, sakamakon wata huduba da ya yi a coci ta tunzura matasan kiristoci a Nsukka da ke jihar Enugu, inda su kai hari a kan musulmai da kuma lalata masallatai.

Shugaban kungiyar Ishaq Akintola, ya ce kungiyar ta goyi bayan Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci, a karar da ta shigar ta na neman a kama tare da gurfanar da Rev. Onah.

Ya ce MURIC ta na da wani faifan bidiyo da Rev. Godfrey ya ke tunzura kiristoci kwanakin da su ka gabata, inda ya ke cewa

Ba zai yiwu a garin Nsukka wasu musulmi su dame su da kiran sallah tun da misalin karfe 4:00 na Asubahi ba.

Ishaq Akintola, ya ce ko shakka babu wannan umarni ne na a yaki musulmi a kuma lalata masallatai a Nsukka, da ma yankin kudu maso gabas gaba daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *