Wata Babbar kotu da ke a Abuja, ta ba babban bankin Nijeriya damar dakatar da asususn ajiyar hukumomi da daidaikun mutanen da ke da nasaba da masu zanga-zangar EndSARS.

Babban bankin ya mika bukatar ne a ranar 20 ga watan Oktoba, kuma kotu ta umurci bankuna da mutane ko kamfanonin ke hulda da masu zanga-zangar su dakatar da asusun ajiyar su har zuwa lokacin da baban bankin zai kammala bincike.

Zanga-zangar EndSARS dai ta yi sanadin tarzomar da ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan Nijeriya, lamarin da ya kada hantar hukumomi.

A sassa da dama na jihohin kudanci da arewacin Nijeriya, an samu matsalar farfasa gidajen ajiyar abincin gwamnati da wasu su ka yi su na kwasar kayan abinci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *