Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Bornon, ya ce zanga-zangar EndSars na iya rikiɗewa zuwa ta’addanci.

Zulum ya shawarci matasa su yi taka-tsantsan wajen neman haƙƙin su game da cin zalun ‘yan sanda, wanda ya ce Boko Haram ma ta fara ne daga zanga-zangar ƙin jinin sa hular kwano ga masu babura.

Zulum ya bayyana wa manema labarai haka ne, jim kaɗan bayan ganawar sa da Shugaba Buhari a Fadar sa da ke Abuja  game da matsalolin tsaro.

“Kun ga yanayin da ake ciki yanzu. Kusan mutum miliyan ɗaya ne suka rasa mahallansu kuma matasa da marasa ƙarfi abin ya fi shafa,” in ji shi.

Ya ce wasu daga cikin waɗanda su ka jagoranci zanga-zangar yanzu haka su na Abuja ko Legas ko kuma ƙasar waje, don haka ya ce wajibi ne akula sosai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *