Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya umarci ‘yan sanda su yi amfani da duk ƙarfin da ya dace domin daƙile tashin hankali da zanga-zanga.

Umarnin dai ya na zuwa ne, yayin da rahotanni ke cewa masu zanga-zangar EndSars su na yunƙurin sake hawa kan tituna.

A wata Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, Mohammed Adamu ya umarci jami’an rundunar kada su ƙyale duk wani tashin hankali domin kare dukiyoyi da rayukan al’umma.

Zanga-zangar EndSars dai an fara ta ne a watan da ya gabata, an kuma dakatar da ita ne bayan ta rikiɗe zuwa tashin hankali a sassa daban-daban, lamarin da ya janyo kisan mutane kusan 80 ciki har da jami’an tsaro.

Tuni dai hukumomi sun rufe asusun ajiyar wasu fitattu daga cikin masu shirya zanga-zangar, an kuma karɓe fasfo tare da hana ɗaya daga cikin su fita daga Nijeriya sakamakon bincike da hukumomi su ka ce su na yi a kan ta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *