Ana ci gaba da kidaya kuri’un da aka jefa na zaben shugaban Amurka a ranar 4 ga Nuwambar 2020 tsakanin shugaban kasa mai ci yanzu na jam’iyyar ‘Republican’ da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na jam’iyyar ‘Democrat’ da kuma a halin yanzu yake gaba da Trump.

Har yanzu ana ta tirka-tirkar neman lashe kuri’un jihohin da ke da karfin tabbatar da wanda zai yi nasara da a ke kira ‘electoral college vote’ a turance. 

Ya zuwa yanzu Jeo Biden ya ci jihohin da ke kasa da suka bada jimillar kuri’a 253 ga Biden daga cikin 270 da yake nema don zama sabon shugaban Amurka.

 1. Maryland – 10
 2. Washington DC – 3
 3. Virginia – 13
 4. Vermont – 3
 5. Massachusetts – 11
 6. Delaware – 3
 7. New York – 29
 8. New Jersey – 14
 9. Colorado – 9
 10. Connecticut – 7
 11. Illinois – 20
 12. New Mexico – 5
 13. California – 55
 14. Oregon – 7
 15. Washington – 12
 16. New Hampshire – 4
 17. Rhode Island – 4
 18. Nebraska – 1
 19. Minnesota – 10
 20. Hawaii – 4
 21. Maine – 3
 22. Wisconsin – 10
 23. Michigan – 16

Shi kuma shugaban kasar kuma dan takarar jam’iyyarsa Donald Trump ya lashe jihohin da ke kasa masu karfin wakilan zaben da suka ba shi yawan kuri’a 214 kamar haka:

 1. Kentucky – 8
 2. Wyoming – 3
 3. Indiana – 13
 4. North Dakota – 3
 5. Oklahoma – 7
 6. Kansas – 6
 7. Alabama – 9
 8. Ohio – 18
 9. Arkansas – 6
 10. Idaho – 4
 11. South Dakota – 3
 12. Luisiana – 8
 13. Tennessee – 11
 14. Mississippi – 6
 15. South Carolina – 9
 16. Texas – 38
 17. Nebraska – 4
 18. Montana – 3
 19. West Virginia – 5
 20. Iowa – 6
 21. Missouri – 10
 22. Florida – 29
 23. Utah – 6

Abin jira a gani shine wa zai lashe kuri’un da a ke ta kiki-kaka a kai na jihohin nan masu karfin wakilan kwalejin zaben da suka hada da Pennsylvania (kuri’a 20), Arizona (kuri’a 11), Georgia (kuria 16), Nevada (kuri’a 6), North Carolina (kuri’a 15) wadanda sune raba gardamar da a ke jira daga nan zuwa gobe ko fiye da gobe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *