Rundunar sojin Nijeriya ta yi ikirarin cewa, za ta murkushe sauran mayakan Kungiyar Boko Haram da na ISWAP daga maboyar su da ke yankin arewa maso gabashin Nijeriya, bayan wasu jerin farmakin ta na baya-bayan nan da ta hallaka tarin mayakan kungiyoyin biyu.

Ma’aikatar tsaron Nijeriya ta ce, a cikin wata guda dakarun rundunar ‘Operation fire ball’ ta yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da na ISWAP 75 a yankin, sai dai ita ma ta yi rashin dakaru 3 da su ka kwanta dama yayin arangamar, baya ga wasu 4 da su ka jikkata.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaron Nijeriya Brigadier Janar Benard Onyeuko, ya ce tsakanin ranar 28 ga watan Satumba zuwa ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka samu wannan nasara.

Ya ce Rundunar bangare daya ne a karkashin Rundunar operation lafiya dole da aka kafa domin kakkabe burbushin ‘yan Kungiyar, ganin yadda su ka yi kaurin suna wajen kai hare-hare a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *