Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, zai mika ragamar shugabancin rikon-kwarya  na hukumar ga wani baturen zabe har sai majalisar tarayya ta tabbatar da sake nadin sa ko akasin haka.

Yayin da wa’adin Farfesa Yakubu zai kare a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, shugaba Buhari ya sake zaben shi tare da mika sunan sa ga majalisar tarayya domin tabbatar da shi.

Ana sa ran Farfesan zai mika ragamar mulkin hukumar ga kwamishinonin da wa’adin su bai kare ba.

A wata sanarwa da Sakataren yada labarai na hukumar zaben  Rotimi Lawrence Oyekanmi ya fitar, ya ce akwai wasu kwamishinoni biyar da su ka yi wa’adi biyu, don haka ba su da damar kara wani wa’adi a kan aikin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *